Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga Gwamnati ta tabbatar ta dauki matakin hukunta duk wadanda aka samu da laifin kisan mafarauta yan asalin Kano a jihar Edo.
Sarkin yayi wannan kira cikin sakon sa na Barka da Sallah, tare da miƙa saƙon jaje da ta’aziyyar rasuwar yan asalin jihar Kano da aka yiwa kisan gilla a jihar Edo.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran Sarkin Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, ya fitar.
Sanarwar tace Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya jikan waɗanda aka kashe ɗin ya kuma karbi shahadar su.
Sannan ya bukaci Gwamnatoci a kowane mataki dasu samar da hanyoyin saukakawa jama’a ƙuncin rayuwa.
Daga karshe ya bukaci mawadata su cigaba da taimako da tallafawa marasa karfi domin samun saukin al’amuran rayuwa na yau da kullum.