Atiku Abubakar ya miƙa saƙon barka da Sallah ga yan Najeriya

0
32

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar PDP a zaɓen shekarar 2023, Atiku Abubakar, yace azumin watan Ramadana na wannan shekara ya zo a lokacin da ake cikin matsananciyar wahala da yunwa a Najeriya.

Yace a yayin da watan Ramadan ya ƙarfafa bayar da sadaka ga marasa ƙarfi, yana da matukar muhimmanci ga shugabanni su tabbatar da cewa sun ɗauki matakan da za su sauƙaƙa wa al’umma wahalhalun da suke ciki.

Atiku ya ƙara da cewa dole ne a jawo hankalin masu rike da madafun iko zuwa ga koyarwar Annabi Muhammad (SAW) wanda ya bayyana nauyin shugabanci akan jagorori.

Cikin sanarwar daya fitar a shafin sa na Facebook Atiku yace ba ya kyautuwa gwamnati ta cigaba da kiran jama’a da su cigaba da nuna juriya akan wahalhalun da suke fama da su, abu mafi dacewa shi ne shugabanni su nuna jinƙai ga talakawa ta hanyar gudanar da mulki da tsoron Allah.

Daga ƙarshe ya roƙi al’ummar musulmi su ɗauki bikin sallah ƙarama a matsayin wata dama ta tunatar da juna muhimmancin ci gaba da ayyukan alheri da aka aiwatar a cikin watan Ramadan, tare da cigaba da addu’a domin ci gaban rayuwa da ƙasa baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here