Sheikh Sudais ne zai jagoranci Sallar Idi a Haramin Makkah

0
76

Mahukuntan ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulrahman Al-Sudais, ne zai jagoranci Sallar Idi a Haramin Makkah a ranar 1 ga watan Shawwal 1446.

Sudais ya kwashe shekaru 40 yana limanci a Saudiyya amma bai taɓa jagorantar Sallar Idi a masallacin Harami ba.

Kafin yanzu Sheikh Saleh Al Humaid, ne ya shafe shekaru 22 a jere yana jagorancin Sallar Idi a masallacin Harami.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here