Sarkin Kano na 15 Aminu Ado, yace gobe ne ƙaramar Sallah

0
60

Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa gobe Lahadi itace ranar 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446 AH.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace kamar yadda aka Samu umarni daga Mai Alfarmar Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar lll an ga jaririn watan Shawwal a garuruwan Borno da Daura da Moru.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran Sarkin Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, ya fitar a daren asabar.

Sanarwar tace bayan tattaunawa da dukkan malamai sun tabbatar da ganin watan na Shawwal, a don haka ne ya umarci al’umma su ajiye azumin Ramadan, don gudanar da shagulgulan Sallah ƙarama.

Daga nan ya tunatar da al’ummar Musulmi muhummacin fitar da zakkar fidda Kai. Ya kuma yi addu’ar Allah ya karbi Ibadu yasa ayi bukukuwan Sallah karama lafiya .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here