Mahara sun kashe mutane 10 a jihar Filato

0
35

Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harin da wasu mahara suka kai wa al’ummar Ruwi da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato.

Maharan sun kai harin ne a daren Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mutanen da suka halarci wata jana’iza da misalin ƙarfe 9:30 na dare.Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar harin, amma ba ta bayyana adadin waɗanda suka rasu ba.Kakakin rundunar, DSP Alabo Alfred, ya ce, Kwamishinan ‘yan sanda ya tura ƙarin jami’an tsaro don wanzar da zaman lafiya.

Tuni dai gwamnatin Jihar Filato ta yi Allah-wadai da harin.Kwamishiniyar Yaɗa Labarai ta jihar, Joyce Ramnap, ta tabbatar wa jama’a cewa ana ɗaukar matakan kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here