Tankar fetur ta faɗi a tsakiyar Kaduna

0
40

Tankar man fetur ta faɗi a tsakiyar Kaduna kan hanyar zuwa gidan Gwamnati.

Kawo wannan lokaci jami’an tsaro sun rufe hanyar shiga tsakiyar Kaduna daga Unguwar Sarki zuwa UTC, tare da zube jami’an kashe gobara domin jiran ko ta kwana.

 Haka zalika an bayar da rahoton cewa jami’an tsaro sun kori wasu mutane da suka je wajen suka fara kwasar man dake kwarara.

Har ila yau an kori ma’aikatan bankin Taj  dake inda lamarin ya faru don gujewa samun matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here