Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta gudanar da hawan Sallah
Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da haka a shafinsa na Facebook.
Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da Sarki Aminu ya soke hawan da ya tsara yi, yayin da gwamnatin Kano ta umurci Sarki Sanusi ya gudanar da bikin al‘adar da ke tara dubban jama’a a cikin Kano.