Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar PDP a zaɓen shekarar 2023 Atiku Abubakar, yayi ala wadai akan kisan gillar da aka yiwa wasu ƴan arewa a Edo.Na shiga cikin tashin hankali bayan samun labarin kisan gillar da aka yiwa wasu ƴan farauta a jihar Edo. Ina miƙa saƙon ta’aziyya ta ga ƴan’uwa da abokan waɗanda abun ya shafa, inji Atiku.
Atiku, ya sanar da hakan cikin wani saƙon daya wallafa a shafin sa facebook.
Yace wannan mummunan al’amari yana buƙatar sahihin bincike domin gano waɗanda suka yi wannan ɗanyen aikin a kuma tabbatar da cewa an ɗauki hukuncin da ya dace akan su.
Atiku ya kuma ce tsaron rayukan mutane abu ne da bai kamata a yi wasa da shi ba, saboda haka, ina kira ga hukumomin da abun ya shafa su ɗau matakin gaggawa domin kare aukuwar ɗaukar doka a hannu irin wannan a nan gaba.
Ya zama dole a tabbatar da adalci domin farfaɗo da yaddar al’uma akan hukumomin tsaron ƙasar nan, a cewar Atiku Abubakar.