An kashe ƴan jihar Kano 16 a jihar Edo

0
120

Matasan jihar Edo sun kashe hausawan jihar Kano da suka taho yin bukukuwan Sallah ƙarama.

Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 16, aka kashe a jiya Alhamis.

Kamar yadda lamarin ya faru a gaban idon wani bahaushe dake rayuwa a inda aka yi kisan, yace mutanen da aka kashe mafarauta ne.

Da farko wasu matasa ne suka tare motar mafarautan inda suka fara bincike, bayan sun samu bindigar mafarauta da karnuka a wajen matafiyan sai suka fara kashe su tare da cewa ƴan garkuwa da mutane ne.

An kashe wasu da makami yayin da aka ƙone wasu ƙurmus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here