Karamin ministan gidaje da cigaban birane Yusuf Abdullahi Ata, ya kaiwa Gwamnan jihar Katsina ziyarar ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar sa Hajiya Safara’u Umar.
Yusuf Abdullahi Ata, yakai ziyarar a jiya Alhamis.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da babban mai taimakawa, karamin ministan a fannin kafafen yada labarai, Adamu Aminu, ya fitar.
A yayin ziyarar ta’aziyyar Ata ya yabawa Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda, bisa yadda ya rayu da mahaifinsa cikin tarbiyya da yi musu biyayya, yana mai cewa hakan babban abu ne mai muhimmanci a addinin Islama.
Ya kuma yabawa Gwamnan akan yadda ya kula da mahaifiyar tasa har zuwa lokacin da ta koma ga Ubangiji, tare da yi mata addu’ar samun rahama.
A nasa jawabin gwamna Radda, ya bayyana jin dadin sa akan yadda karamin ministan yakai masa ziyarar ta’aziyyar.