Sarki Aminu Ado Bayero ya janye hawan Sallah ƙarama

0
70

 Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ta dakatar da tsarin bikin hawan sallah karama.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar da hakan Yana Mai bayyana cewa yin hakan ya biyo bayan wasu dalilai.

Yace bayan samun shawarwari da kiraye kiraye daga shugabanni da iyaye da Malamai da Kuma tattaunawa da yan Majalisar Sarki ya zama wajibi a dakatar da hawan Sallah Karama na wannan shekara.

Sarkin yace Hawan Sallah ba abune na ko a mutu ko ayi rai ba, Wanda idan yin hakan zai kawo tashin hankali ko hargitsi da kawo rashin zaman lafiya to ya zama wajibi a hakura da yin hawan.

Akan haka ne  Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’uma da sauran masoya suyi hakuri da wannan hukunci da aka zartar domin samun dorewar zaman lafiya a jihar Kano da kuma kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here