Wani matashi dan shekara 25 mai suna Joseph Abodunrin ya kashe kansa a unguwar Dagbolu da ke karamar hukumar Osogbo ta jihar Osun sakamakon tsadar rayuwa a ƙasa, lamarin da ya yi ikirarin cewa yana dagula masa lafiyar kwakwalwa.
Jaridar VANGUARD ta rawaito cewa ƴar uwar mamacin, Abodunrin Grace ce ta tabbatar da mutuwarsa a yau Alhamis a shafin ta na X.
A cewar matar da ta bayyana shi a matsayin ɗan uwan ta da take matuƙar kauna, Joseph ya kasance mai ɓoye duk radadi cikin murmushi, yana mai nuna cewa komai ya yi daidai, tare da karfafa musu gwiwa.
Kafin mutuwar ta sa, an ruwaito cewa Joseph ya wallafa saƙonni a shafin X na barazanar kashe kan nasa.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Osun, ASP Akeem Adeoye, ya shaida cewa bai san da faruwar lamarin ba.