Sheikh Abdulrahman Al-Sudais zai jagoranci Sallar Tahajjud ta yau

0
178

Sheikh Abdulrahman Al-Sudais, ne zai jagoranci Sallar Tahajjud a masallacin Haramin Makkah a daren wannan rana ta 26 ga watan Ramadan da akafi kyautata zaton dacewa da Lailatul Qadr.

Babban limamin zai kuma jagoranci gabatar da addu’o’in nemawa musulmai dacewa, da nemawa duniya samun zaman lafiya da sauran su.

Shafin Inside Haramai dake bayyana abubuwan dake faruwa a Haramin Makkah da Madina ne ya sanar da hakan cikin sakon daya wallafa a shafin Facebook.

Manyan masana addinin Musulunci dai na jan hankalin al’umma su dage da yin addu’o’in neman dacewa da inganta ibadun su a kwanaki 10 na Æ™arshen watan Ramadan musamman a wannan dare na 27 ga watan don neman daren Lailatul Qadr mai alkairi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here