Rundunar sojin Najeriya ta sanar da tura jami’an ta 171 zuwa yankin Abyei dake kan iyakar kasashen Æ™asar Sudan da Sudan ta Kudu, don yin aikin kwantar da tarzoma.
Shugaban sashin ayyuka na rundunar Manjo Janar Boniface Sinjen, ne ya sanar da haka a wajen bikin yaye sojojin Najeriya na 3 na Majalisar Dinkin Duniya a Cibiyar Shugabanci da Zaman Lafiya ta Duniya ta Martin Luther Agwai (MLAILPKC), dake Jaji a jihar Kaduna, wanda aka gudanar a ranar Talata.
Sinjen wanda shine babban baƙo mai jawabi a wajen taron ya shaidawa dakarun da aka yaye cewa su shirya tafiya yankin Abyei, karkashin shirin majalisar dinkin duniya na UNISFA.
Yace manufar hakan shine a tabbatar da cewa aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin bai tsaya akan harkokin soji kaÉ—ai ba, sai dai ya Æ™unshi harkokin diflomasiyya da sauran al’amuran rayuwa.