Bani da tabbacin tsayawa takara a 2027—Atiku Abubakar

0
73

Tsohon Mataimakin Shugaban Æ™asa kuma tsohon É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyar PDP a shekarar 2023, Atiku Abubakar, yace bashi da tabbacin tsayawa takarar shugaban Æ™asa a kakar zaÉ“e mai zuwa ta 2027.

Atiku, ya sanar da hakan lokacin da aka yi wata ganawa da shi wadda ba’a kai ga yaÉ—a ta ba, amma jaridar Daily trust ta samu bayanan abin da tattaunawar ta Æ™unsa.

Atiku Abubakar, yayi ganawar ce tare da Adesuwa Giwa-Osagie, da ake kyautata zaton za’a yaÉ—a hirar a yau Laraba.

A kwanakin nan ne Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa suna yin wata haɗakar da zata sanya ƴan adawa kwace kujerar shugabancin ƙasa daga hannun Tinubu a 2027.

Sai dai har yanzu babu tabbas akan wanda zai jagoranci tawagar haÉ—akar a tsakanin Atiku Abubakar, Peter Obi, ko kuma El-Rufa’i.

A lokacin da aka tambaye shi ko zai tsaya takara a shekara ta 2027, Atiku Abubakar yace bashi da tabbacin hakan.

Atiku Abubakar dai ya tsaya takarar neman shugabancin Nijeriya har sau 6.

A yayin zantawar Atiku ya amince da kalaman tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, wanda ya ƙalubalanci yanayin tafiyar da dimokuraɗiyyar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here