An rushe ginin dake jikin Ƙofar Ɗan-Agundi

0
77

An wayi gari da ganin an rushe ginin dake jikin Ƙofar Ɗan-Agundi wanda tsohuwar gwamnatin Kano karkashin Ganduje ta raba shi ga wasu mutane.

Sai dai har yanzu ba’a ji ko wace hukuma ce ta rushe ginin ba.

Rahotanni sun bayyana cewa maganar takaddamar filin da aka rushe na gaban Kotu.

Mazauna unguwar da akayi rusau din sunce sun hangi jami’an tsaro da manyan makamai lokacin da aka zo rushe ginin a cikin daren Talata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here