Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar PDP a shekarar 2023 yace bai yi mamakin yadda majalisun dokokin ƙasa suka amince da dokar ta ɓacin jihar Rivers ba.
Atiku Abubakar, yace hakan ya faru sakamakon yadda cin hanci da rashawa ya mamaye shugabancin majalisar.
Atiku Abubakar, jaddada cewa babu gudu ba ja da baya tabbas akwai cin hanci da rashawa a majalisun dokokin ƙasa saboda yana da tabbacin hakan. Sannan yace ƴan majalisar zasu iya aikata komai.
Ɗan takarar yace yanzu shine lokacin da Najeriya ke bukatar samun shugabanci na gari fiye da lokutan da suka wuce.
Atiku ya sanar da hakan cikin wata ganawar da akayi dashi, wadda za’a yaɗa a yau Laraba.