Majalisar wakilai tayi karatu na biyu akan ƙudirin cire rigar kariga daga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni
Kudurori akalla 42 ne suka tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilan ciki har da kudurin cirewa mataimakin shugaban kasa da gwamnoni har ma da mataimakansu rigar kariya domin fuskantar shari’a kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.
An samar da kudirin ne don dakile cin hanci da rashawa, kawar da rashin adalci, da kama karya da wasu gwamnoni ke yi.