Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi ll, ya yi kira ga al’umma da su kasance masu bin doka, su zauna lafiya, su hada kai don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa da ya ke jawabi a wurin taron buɗe-baki na musamman a fadarsa a ranar Lahadi, Sarkin ya soki masu adawa da dawowarsa kan karagar mulki, inda ya bayyana cewa “wuta za ta cinye masu tayar da zaune tsaye a cikin birnin Kano.”
Sanusi ya kara da cewa, waɗanda ke kalubalantar sarautarsa jayayya suke yi da ikon Allah, inda ya ce za su “fuskanci sakamako mai muni domin sun bijirewa abin da Allah Ya ƙaddara.
Sarki Sunusi yace ayi hakuri a ci gaba da yin addu’a, domin Allah na tare da mai gaskiya.
Yace tabbas wanda ya ƙalubalanci hukuncin Allah ba zai taɓa cin nasara ba.
Jawaban Sanusi sun biyo bayan umarnin Gwamnan Kano, na cewa masarautu su fara shirin Hawan Sallah, a daidai lokacin da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero, shi ma ya sanar da hukumomin tsaro shirinsa na gudanar da Hawan da kuma bikin cika shekaru biyar a matsayin Sarkin Kano.