Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya janye hannunsa daga sauraron shari’ar da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio.
A zaman kotun a yau Talata, Alkali Egwuatu ya bayyana matsayarsa ta janyewa daga shari’ar bayan gabatar da kara a kotun tasa kamar yadda aka saba.
Ya ce babban dalilin da ya sa ya janye shi ne zargin nuna son kai da aka yi masa daga wanda ake kara na uku a shari’ar, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana rashin amincewarsa da ikon kotun Egwuatu, wajen yin adalci a lamarin, wanda hakan ya kai ga janyewar alkalin.
Egwuatu ya kara da cewa za a mayar da kundin shari’ar ga Babban Alkalin Babbar Kotun Tarayya, John Tsoho, domin sake tura shari’ar ga sabon alkali.