Kotuna suna yiwa jam’iyyun adawa zagon ƙasa—Shugaban SDP

0
24

Shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa Shehu Gaban, yace ana haɗa baki da kotuna wajen yiwa jam’iyyun adawa da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC zagon ƙasa.

Gabam yace hakan abin takaici ne yadda kotunan ke shiga harkokin jam’iyyun siyasa da INEC.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana hakan a ranar Litinin lokacin da yake zantawa da tashar talabijin ta Channels.

Gabam yace burin sa shine su kafa jam’iyya irin ANC ta ƙasar Afrika ta Kudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here