Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a jihar Rivers sun yi barazanar fara aiwatar da ayyukan da za su kawo cikas ga harkokin tattalin arzikin kasa matukar shugaba Bola Tinubu bai janye dokar ta-baci da aka sanya wa jihar ba.
Kungiyoyin kwadagon sun sanar da hakan cikin wata sanarwar da suka fitar ta haɗin gwuiwar,inda suka ce dokar ta ɓacin ta kawo matsala a yanayin biyan ma’aikata albashi.
Idan za’a iya tunawa a ranar 18 ga watan Maris ne shugaban ƙasa Tinubu ya dakatar da gwamna Siminalaya Fubara da mataimakiyar sa tare da dakatar da majalisar dokokin jihar Rivers biyo bayan rikicin siyasa.
Shugaban ya sanar da naɗin Ibok Ete Ibas, a matsayin gwamnan riƙon ƙwarya.