Kotun ɗaukaka ƙara ta sake ɗage sauraron shari’ar zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano.
Kotun ta ce sai ranar takwas ga watan Afrilu mai kamawa za ta sake zama kan karar.
Jam’iyyar NNPP ce dai ta shigar da karar inda ta ke kalubalantar hukuncin Babbar Kotun Tarayya dake Kano wacce ta rushe zaben.