Bani da alaƙa da masu fasa bututun man Najeriya—Fubara

0
31

Dakataccen gwamnan jihar Rivers Siminalaya Fubara yace bashi da wata alaƙa tsakanin sa da tsageru masu fasa bututun man fetur na Najeriya, kamar yadda wasu ke yin zargi.

Yace babu gaskiya a wasu hotuna da bidiyo da ake yadawa da sunan yana da alaƙa da tsagerun.

Ya ce ana yaɗa labaran ƙaryar ne domin a tayar da zaune tsaye a Rivers sannan a ɓata masa suna.

Fubara ya bayyana haka ne a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi ya fitar, inda ya ce Fubara na alla-wadai da yada labaran da bana gaskiya ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa Fubara ba zai taɓa haɗa kai da masu ƙoƙarin kawo koma bayan tattalin arzikin Rivers ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here