Wasu daga cikin mutanen mazabar Kogi ta tsakiya sun miƙawa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC buƙatar yiwa Natasha Kiranye daga Majalisar dattawa.
Bisa tanadin doka dole sai kaso 50 na adadin mutanen da suka yi zabe sun amince da yin Kiranyen tare aikawa shugaban hukumar INEC bukatar su.
Tun a makon daya gabata ne aka fara karɓar ra’ayin al’ummar mazabar Kogi ta tsakiya da nufin yiwa Natasha Kiranye, bisa zargin ta da rashin yin abinda ya kamata a wakilcin ta.
Natasha dai na cigaba da fuskantar kalubale tun bayan da ta zargi shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da yunƙurin yin lalata da ita.