Jami’an tsaron sa kai 10 sun mutu a hannun ƴan ta’addan Zamfara

0
30

Ƴan bindiga sun kashe jami’an tsaron sa kai 10 a jihar Zamfara lokacin da suka far musu da harin kwanton ɓauna a ranar Asabar.

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya ce shida daga cikin wadanda aka kashe dakarun tsaron gwamnatin jihar ne da ake kira Askarawa, huɗu kuma ‘yan sa-kai ne.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya ƙara da cewa akwai dakarun Asakarawa biyu da ɗan sa-kai ɗaya da suka ɓata yayin harin.

A cewar gwamnan lamarin ya faru bayan farmakin da gamayyar jami’an tsaro ciki har da Askarawa ƙarƙashin jagorancin sojojin Najeriya suka kai wa sansanin ‘yan bindiga a dajin Sunƙe, wanda aka samu gagarumar nasarar kashe ƴan bindiga tare da ƙwato makamai.

Ya ce tuni aka yi jana’iza mamatan a yau Lahadi, yana mai cewa ya bayar da umarnin ɗaukar matakin bayar da agajin gaggawa ga waɗanda suka ji raunuka da kuma bayar da tallafin gaggawa ga iyalan waɗanda suka rasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here