An saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya lokacin da Majalisa ta amince da dokar ta ɓacin jihar Rivers—Tambuwal

0
19

Tsohon Gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya ce Majalisar Dattawan ƙasa ba ta samu adadin ƴan majalisun da ake buƙata ba, wajen amincewa da dokar ta bacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanya a Jihar Rivers.

Tambawal ya shaidawa Jaridar The Sun cewar, adadin ƴan majalisun da suka halarci zaman ba su kai 73 ba, daga cikin 109 da ake da su.

 Saboda haka Sanatan ya ce matakin da majalisar ta dauka ya sabawa sashi na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

 Wasu ƴan majalisar da kuma masu sanya ido na ci gaba da korafi akan hanyar da aka bi wajen amincewa da dokar, musamman hana ƴan majalisun kaɗa kuri’a ɗaya bayan ɗaya. 

Tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jinjinawa Majalisun ƙasar guda biyu saboda goyan bayan kudirin da ya gabatar musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here