Shugabannin jamhuriyar Nijar sun bayar da hutun kwanaki 3 don jimamin rasuwar mutane 43 da ƴan bindiga suka kashe a ranar juma’ar data gabata lokacin da suke gudanar da Sallah.
Rahotonni sun bayyana cewa harin ya jikkata mutum 13, huɗu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali a harin da aka kai a garin Kokorou da ke kan iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso.
BBC ta rawaito cewa wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijar Mohamed Toumba ya fitar ta ce maharan da ke biyayya ga ƙungiyar (ISGS) ne suka kai harin.
Ministan yace an kai harin da misalin karfe 2 na rana lokacin da ake gudanar da Sallar Juma’a, inda maharan suka ragaye masallacin.
Mayakan sun kuma bankawa gidaje da kasuwa wuta.
Kwana biyu kafin wannan hari rundunar sojin Nijar ta ce ta kashe mambobin ISGS 45.