Gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananun hukumomin sun raba Naira triliyan 1.678

0
36
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananun hukumomin Najeriya sun raba Naira triliyan 1.678, a matsayin kuɗin shigar da aka tattara a watan Fabrairu.

Daraktan yaɗa labarai na ofishin babban akanta na tarayya Bawa Mokwa ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar.

Yace an bawa ƙananun hukumomi Naira biliyan 5.057, jihohi Naira biliyan 562.195, sai gwamnatin tarayya ta karɓi Naira biliyan 569.656.

Adadin ya kasance kuɗin da ake rarrabawa gwamnatocin bayan tattara kuɗin shigar da Najeriya ke samu, tare da ajiyewa a asusun gwamnatin tarayya.

Ana yin amfani da kuɗaɗen wajen tafiyar da ayyukan gwamnati a kowanne mataki da kuma biyan albashin ma’aikata a kowane wata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here