Gwamna Abba ya bayar da aikin yi ga ɗaliban da gwamnatin Kano ta kai Indiya

0
55

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayar da aiki yi ga dalibai 53, da gwamnatin sa ta dauki nauyin karatun digirin su na biyu a kasar Indiya.

Gwamnan ya sanar da hakan a yammacin Juma’a lokacin da ya shiryawa ɗaliban liyafar cin abinci bayan dawowarsu gida Najeriya sakamakon kammala karatun.

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya ce gwamnati zata bawa daliban takardunsu na naukar aiki yace tabbas al’umma na  bukatar gudunmawar su musamman kasancewar mafi yawan daga cikin su sun karanta fannonin kiwon lafiya. Inda yace nan bada jimawa ba za a tura su asibitoci daban daban domin fara aiki.

Ya kuma nemi daliban su yiwa al’ummar jihar Kano sakayya ta alkairi saboda da  kuɗin al’umma aka ɗauki nauyin karatun nasu.

Ya kuma yabawa ɗaliban bisa kwazo da jajircewa da suka nuna wanda ya kai su ga samun kyakkyawan sakamako.

Haka zalika ya bawa kowanne ɗalibi kyautar Naira dubu 100.

Daliban wanda dukkanin su sun kammala Digirinsu na biyu a Jami’ar Symbiosis dake Kasar India sun bayyana godiyarsu akan alkairan da gwamnatin Kano ya yi musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here