Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ya musanta zargin bawa ƴan majalisa cin hancin dala dubu 15, saboda su amince da dokar ta ɓacin jihar Rivers.
Akpabio, yace babu ƙamshin gaskiya akan zargin da wasu keyi na cewa an rabawa mambobin majalisar cin hancin dala dubu 15 don sahalewa shugaban ƙasa Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta ɓaci a Rivers, da kuma dakatar da gwamna Siminalaya Fubara tsawon watanni 6.
Sannan ya nemi al’umma suyi watsi da jita jitar.