An kashe matashi ɗan shekaru 23 a masallaci a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru a unguwar Layin Bilya, dake Makwa a Rigasa, lokacin da ake gudanar da Sallar Tahajjud a ranar Alhamis cikin dare.
Zuwa yanzu jami’an tsaro sun Kama Mutane 12 da ake zaton suna da hannu a kisan don gudanar da bincike.
Rundunar ƴan sandan Jihar ta tabbatar da faruwar kisan ta bakin kakakin ta DSP Mansir Hassan, wanda yace an kira su da misalin karfe 2 na daren ranar 21 ga watan Maris tare da bayyana musu abinda ke faruwa.
A cewar DSP Mansur, rundunar ‘yansandan ta samu rahoto daga wani mazaunin yankin Rigasa cewa ‘yandaba ɗauke da makamai na shirin kai hari kan masu sallar Tahajjud.