Ƴan majalisar dattawan da suka ƙalubalanci ƙaƙabawa al’ummar jihar Rivers dokar ta ɓaci a majalisa.
Daga cikin su akwai Henry Dickson, dake wakiltar yammacin jihar Bayelsa, sai Aminu Tambuwal da Enyinnaya Abaribe.
Mutanen sun fito fili sun bayyana ƙin goyon bayan sanya dokar ta ɓaci a jihar Rivers da kuma dakatar da gwamna Siminalaya Fubara da mataimakiyar sa da shugaban ƙasa Tinubu yayi lokacin da ake tafka muhawara a zauren Majalisar dattawa.
Daga bisani majalisar ta amince da dokar.