Babu abinda zai hana Tinubu samun nasara a zaɓen 2027—Ganduje

0
18

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta hana Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu lashe zaɓen 2027.

Ganduje ya yi wannan jawabi ne domin mayar da martani ga sabuwar haɗakar ’yan adawa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da wasu shugabanni suka kafa.

A yayin taron manema labarai da Atiku ya gudanar a Abuja a ranar Alhamis, ya soki yadda Tinubu ke tafiyar da mulki, musamman batun ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, da wasu ’yan siyasa sun halarci taron inda suka bayyana shirin haɗa kai domin karɓe mulki daga Tinubu a 2027.

Sai dai Ganduje ya yi watsi da wannan yunƙuri, inda ya bayyana cewa tafiyar ba za ta yi tasiri ba.

Ya ce irin nasarorin da Tinubu ya samu tun bayan hawansa mulki ne zai tabbatar da nasararsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here