Ana neman gudunmawar jini don tallafawa mutanen da hatsarin Abuja ya rutsa da su

0
24

Hukumar kula da tattara jini ta ƙasa  NBSA ta nemi al’umma musamman mazauna birnin Abuja dasu taimaka su bayar da gudummawar jini domin tallafa wa mutanen da hatsarin babbar mota ya ritsa da su a babbar hanyar zuwa Keffi.

Lamarin ya afku bayan da motar simintin Dangote ta kama da wuta tare da afkawa motocin da ke gefen titi a ranar Laraba.

Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum shida, wasu 25 sun ji rauni a daidai lokacin suke yin jinya a asibitoci daban-daban.

Hukumar NBSA tace hatsarin mai muni ya ritsa da mutane da dama, waɗanda ke buƙatar ƙarin jini da gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here