An rantsar da Netumbo a matsayin shugabar Namibia mace ta farko

0
39

An rantsar da Netumbo Nandi-Ndaitwah a matsayin shugabar ƙasar Namibia, mace ta farko.

Netumbo Nandi-Ndaitwah, ta kasance tsohuwar ministar harkokin wajen ƙasar a jam’iyyar SWAPO wadda ke mulkin Namibia tun bayan samun ƴancin kai daga Afirka ta Kudu a 1990.

Da take magana da BBC, Nandi-Ndaitwah ta tabbatar da cewa wasu za su iya sukarta saboda jinsinta maimakon ayyukan da take yi , sai dai ta ce za ta ci gaba da yaƙi da cin zarafin jinsi.

Netumbo ta shiga cikin jerin matan Afirka ƙalilan da suka jagoranci ƙasarsu tun lokacin da Liberia ta zaɓi shugabar ƙasa mace ta farko shekaru 20 da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here