Tinubu ya yiwa kundin tsarin mulkin kasa karan tsaye—Atiku da Peter Obi

0
24

Tsaffin yan takarar shugabancin kasa na jam’iyyun PDP da LP a zaben shekarar 2023 Atiku Abubakar da Peter Obi, sun roki mambobin majalisar wakilai su kalubalanci dokar ta bacin da shugaban kasa Tinubu ya sanya a jihar Rivers.

Yan takarar sun nemi hakan a yau Alhamis lokacin da suka gudanar da wani taron manema labarai a cibiyar Yar’adua dake birnin tarayya Abuja, sunce Tinubu yayi karan tsaye ga sashi na 305 na kundin tsarin mulkin kasa wajen sanya dokar.

:::Tinubu Atiku Obi Tattalin arziki

Aiku da Obi, sun nemi Tinubu da ya gaggauta mayar da zababben gwamnan Rivers kan mukamin sa ba tare da bata lokaci ba. Atiku Abubakar shine ya jagoranci tattaunawar a matsayin wanda ya wakilci yan adawa a kalubalantar gwamnatin tarayya wajen sanya dokar.

Sai dai tuni Majalisar wakilai ta fara tafka muhawara akan dokar ta bacin.

Shugaban majalisar Tajuddeen Abbas ne ya karanta wasikar da shugaban kasa Tinubu ya aikewa majalisar inda yake neman ta amince masa sanya dokar.

Bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasa sai kaso 2 cikin 3 na yan majalisun dokokin kasa sun amince da sanya dokar sannan ta zama wadda bata ci karo da doka ba.

A ranar talata da yammaci shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Rivers tare da dakatar da gwamnan jihar Siminalaya Fubara da mataimakiyar sa.

Zuwa yanzu dai tuni majalisar ta amince da sanya dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here