Shugaban Hukumar kula da masallatai Harami Sheikh Dr. Abdulrahman Al-Sudais, ya taya al’ummar musulmi murnar shigowa kwanaki goman ƙarshe na watan Ramadan, inda yayi addu’ar Allah ya karɓi ibadun al’ummar musulmi.
Sheikh Dr. Abdulrahman Al-Sudais, ya miƙa godiyar tasa a yau Alhamis bayan kammala Sallar Isha.
Shehin malamin na ƙasar Saudiyya ya roƙi Allah da ya haɗa ƴan uwa musumai da alkairan dake cikin kwanakin musamman dacewa da ganin daren Lailatul Qadr, da dacewa da yin addu’a a cikin sa.
Sudais, ya kuma nemi musulmai su dage da yin ibada a waɗannan kwanaki masu girma, tare da roƙon waɗanda suka ziyarci ƙasar Saudiyya su bawa hukumomi haɗin kai don magance matsalolin cunkoson mutane a masallacin Harami.