Majalisar wakilai ta fara tafka muhawara akan dokar ta bacin da shugaban kasa ya sanya a jihar Rivers.
Shugaban majalisar Tajuddeen Abbas ne ya karanta wasikar da shugaban kasa Tinubu ya aikewa majalisar inda yake neman ta amince masa sanya dokar.
:::Ana shirin kama Sanata Natasha
Bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasa sai kaso 2 cikin 3 na yan majalisun dokokin kasa sun amince da sanya dokar sannan ta zama wadda bata ci karo da doka ba.
A ranar talata da yamaci shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Rivers tare da dakatar da gwamnan jihar Siminalaya Fubara da mataimakiyar sa.