Majalisar kula da harkokin shari’a ta kasa NJC ta musanta rahoton dake cewa an saki jagoran masu rajin kafa kasar Biapra (IPOB) Nnamdi Kanu, daga gidan gyaran hali, tare da sakin sa zuwa Kasar Kenya.
:::Tinubu ya yiwa kundin tsarin mulkin kasa karan tsaye—Atiku da Peter Obi
NJC ta sanar da hakan a yau Alhamis cikin wata sanarwar data fitar mai dauke da sanya hannun daraktan yada labaran ta Kemi Ogedengbe, a birnin tarayya Abuja, yana mai cewa babu gaskiya a cikin rahoton sakin.
Majalisar tace ana danganta sakin ga babbar mai shari’a ta kasa Kudirat Kekere-Ekun, inda tace babu wata kotun da ta yanke irin wancan hukuncin dake cewa Nnamdi Kanu, ya bar Najeriya.
Kanu dai yana fuskantar tuhume-tuhume 7 da gwamnatin tarayya ke zargin sa da aikata cin amanar kasa, kuma har yanzu yana tsare a gidan gyaran hali na Kuje.