Majalisar dattawa ta amincewa shugaban ƙasa Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Rivers.
Majalisar ta amincewa bukatar shugaban ƙasar lokacin da ta gudanar da wani zaman sirri a yau Alhamis.
Tuni itama majalisar wakilai ta sanar da yarjewa Tinubu sanya dokar bayan da mafi yawan mambobin majalisar suka bayyana amincewa da dokar da kuma sanya gwamnan riƙon ƙwarya a Rivers.