Ibok Ibas ya shiga fadar gwamnatin jihar Rivers

0
56

Gwamnan riƙon ƙwarya na jihar Rivers Vice Admiral Ibok Ete Ibas, ya shiga fadar gwamnatin jihar a yau Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa ya shiga ganawar sirri da manyan jami’an tsaron jihar, wakilan gwamnatin tarayya, da kuma manyan jami’an gwamnatin Rivers.

Hakan yazo a daidai lokacin da Majalisar wakilai ta amince da sanya dokar ta ɓaci a jihar, tare da sanya gwamnan riƙon ƙwarya.

Idan za’a iya tunawa a yammacin Talata data gabata shugaban ƙasa Tinubu ya ayyana sunan Ibok Ibas, a matsayin gwamnan riƙon Rivers bayan dakatar da gwamna Siminalaya Fubara da mataimakiyar sa tsawon watanni 6.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here