Gwamnan Kano ya ƙarawa ma’aikatan makarantun gaba da Sakandire albashi

0
74

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da ƙarin kaso 25 da 35 na albashi ga ma’aikatan makarantun gaba da Sakandire masu koyarwa da waɗanda ba malamai ba, wanda ƙarin zai fara aiki daga watan Maris na 2025.

Kwamishinan yaɗa labarai Ibrahim Abdullahi A Waiya, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis lokacin da yake zantawa da manema labarai akan abubuwan da aka cimma lokacin taron majalisar zartarwa ta Kano.

Waiya yace anyi ƙarin saboda irin gudunmawar da ma’aikatan suke bayarwa wajen cigaban ilimi a Kano baki ɗaya.

Ya kara da cewa majalisar ta amince a kashe Naira biliyan 3.3 don yin ayyukan cigaban al’umma a faɗin jihar Kano, da kuma Naira miliyan 148.7, da za’a yi aikin gyara titin zuwa makarantar Fasaha ta jihar Kano (SOT).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here