Atiku zai jagoranci haɗakar kawar da gwamnatin Tinubu a 2027

0
31

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a shekarar 2023 Atiku Abubakar zai jagoranci haɗakar kawar da gwamnatin Tinubu a 2027.

Atiku, ya sanar da hakan a yau lokacin daya jagoranci haɗakar ƴan adawa don kalubalantar ƙaƙabawa al’ummar jihar Rivers dokar ta ɓaci da gwamnan riƙon ƙwarya.

An gudanar da taron a Cibiyar Shehu Musa Yar’adua da ke birnin tarayya Abuja.

Taron ya haɗar da ƴan siyasar adawa na jam’iyyu da dama cikin su har da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i.

Ɗan takarar shugaban ƙasar na PDP a shekarar 2023 ya tabbatar da cewa haɗakar tasu zata zamo wata hanyar kawar da Tinubu daga mulkin Najeriya a shekarar 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here