An sake buɗe ofishin jakadancin Amurka dake jamhuriyar Nijar, bayan da aka rufe shi na tsawon lokaci.
Buɗewar ta ƙunshi dawo da ɗaukacin ayyukan da aka dakatar da gudanarwa a baya.
A yanzu jami’an diflomasiyyar Amurka dake Nijar zasu cigaba da yin ayyukan bayar da bisa ga matafiya.
Sanarwar da ofishin ya fitar a ranar Laraba ta ce za a ci gaba da ayyukan jakadanci da suka haɗa da aiwatar da aikin biza, ayyukan da suka shafi Amurkawa mazauna Jamhuriyar Nijar, da taimakon Amurkawa da masu neman bizar Amurka a Nijar.
Ofishin Jakadancin ya sha alwashin jajircewa wajen samar wa jama’a ayyuka masu inganci da tsaro.