Masu yin sana’a a kasuwar hatsi ta duniya dake Dawanau, da mazauna garin sun gudanar da zanga-zanga akan yadda suka ce an gaza biyan su abin da ya kamata a diyyar guraren su da aikin titin jirgin ƙasan Kano Zuwa Maradi ya shafa, wanda tuni aka rushe wasu guraren.
An gudanar da zanga-zangar a wajen da aikin titin ke gudana, yayin da mutanen ke neman ɗauki, lokacin da suke dauke da kwalaye a hannun su masu nuna ƙalubalantar rashin biyan su abin da ya kamata.
Shugaban masu shirya zanga-zangar Nura Muhammad, yace mafi yawancin mutanen da abin ya shafa an tura musu diyyar da bai taka kara ta karya ba.
Sannan yace wasu ma ba’a biya su ko sisi ba a daidai lokacin da masu aikin suka shirya rushe ƙarin wasu gidajen.
Akan haka ne suke kira ga shugaban ƙasa Tinubu, da mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril, da sauran masu ruwa da tsaki su kawo musu ɗauki.