Tinubu ya aikata lefin da za’a iya tsige shi—Barrister Abdulƙadir

0
33
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Barrister Abdulƙadir A. Sani masanin harkokin shari’a mai zaman kansa ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya aikata babban kuskure wajen ayyana dokar ta ɓaci, da dakatar da gwamna Siminalaya Fubara da mataimakiyar sa a jihar Rivers.

Masanin harkokin shari’ar ya bayyana hakan a yau Laraba lokacin da yake zantawa da Daily News 24 Hausa.

Lauyan yace bangaren Shari’a bai gaza wajen magance rikicin Rivers ba, amma kwatsam aka ji shugaban ya ayyana dokar ta ɓaci duk da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai bayar da damar ɗaukar irin wannan babban mataki ba.

Abdulƙadir yace da ana bin ƙa’ida abu ne mai sauki majalisar dokokin ƙasa ta iya tsige shugaban ƙasa akan abin daya aikata a Rivers.

Ya ƙara da cewa a baya an saka dokar ta ɓaci a jihohin Adamawa Borno da Yobe, amma ba’a dakatar da gwamnoni ba duk da cewa ana kisan mutane. Sannan yace siyasa ta taka rawa akan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.

A. Sani, yace sashi na 305, na kundin tsarin mulkin kasa da shugaban ƙasa yayi amfani da shi wajen sanya dokar ta ɓaci a Rivers ba’a yi amfani dashi ta hanyar data dace ba, saboda ana yin amfani da shi in za’a ci Najeriya da yaƙi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here