Shugaban ƙasa Tinubu ya aikata irin abinda ya ƙalubalanci tsaffin shugabannin Najeriya Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, da aikata dangane da sanya dokar ta ɓaci a jihohi.
Idan za’a iya tunawa a shekarar 2004, ya ƙalubalanci Obasanjo kan yadda ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Filato a ranar 18 ga watan Mayu.
Bayan haka ya kalubalen tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, yayin da ya ayyana dokar ta ɓaci a jihohin Adamawa, Borno da Yobe, a ranar 14 ga watan Mayu na shekarar 2013.
Sai gashi a jiya 18 ga watan Maris, Tinubu ya saka dokar ta ɓaci a jihar Rivers, tare da dakatar da gwamnan jihar zaɓaɓɓe Siminalaya Fubara, da mataimakiyar sa.