Sabon kwamishinan ƴan sandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori Phd, ya kai ziyara kasuwar Kwalema dake unguwar Dakata, ta ƙaramar hukumar Nasarawa inda aka samu tashin gobara.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta ƙone wajen da ake yin gwangwan din robobi na kasuwar.
Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da hakan cikin wani saƙon daya fitar a shafin sa na Facebook.
Gobarar ta kone shaguna da dama, wanda hakan ya janyo asarar dukiyar da ba’a san adadin ta ba.
Kwamishinan yan sandan yakai ziyarar a yau Laraba da rana inda ya ganewa idon sa irin ɓarnar da gobarar tayi, tare da umartar gudanar da bincike don sanin dalilin tashin gobarar.