Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa zata aikawa Vice Admiral Ibok Ete Ibas, kason kuɗin jihar Rivers na ƙasa, bayan dakatar da gwamnan jihar zaɓaɓɓe.
Ministan Shari’a Lateef Fagbemi, ne ya sanar da hakan ga manema labarai lokacin da suke zantawa da shi a fadar shugaban ƙasa dake birnin tarayya Abuja.
Yace gwamnan riƙon yana da ikon neman kuɗi daga gwamnatin tarayya don aiwatar da ayyuka.
Fagbemi, yace shugaban ƙasa Tinubu ya ɗauki matakin sanya dokar ta ɓaci a Rivers don magance samun rikice rikicen siyasar da jihar ta afka.
A kwanakin baya kotun ƙoli ta zartar da hukuncin dakatar da turawa jihar Rivers kason kuɗin ta na gwamnatin tarayya har zuwa lokacin da za’a magance matsalolin kasafin kuɗin jihar tsakanin Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike.